Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Geng Shuang, ya furta a yau Laraba cewa, ta la'akari da yanayin da duniya ke ciki, yadda wadannan kasashe masu makaman nukiliya suka zauna tare, domin musayar ra'ayi kan al'amura masu alaka da tsaro, wani sako ne mai kyau ga daukacin al'ummomin duniya.
Babban jigon da ake tattaunawa a kai wajen taron shi ne " kara hadin kai don kiyaye tsarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya". Sa'an nan kasashen 5, za su yi tattaunawa mai zurfi kan manufofi masu alaka da makaman nukiliya, da rage makaman, da hana yaduwarsu, gami da yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana, da dai makamantansu. (Bello Wang)