in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane biyu sun mutu a sakamakon harin da aka kai ga tashar mai dake babban birnin kasar Somaliya
2019-01-30 15:54:31 cri
Wani jami'in kasar Somaliya ya bayyana a ranar 29 ga wata cewa, an kai harin bom da aka ajiye a cikin mota a wani gidan mai dake birnin Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya a safiyar wannan rana, wanda ya haddasa mutuwar mutane 2 tare da raunatar mutane 5.

Wadanda suka ganewa idonsu faruwar lamarin sun bayyana cewa, fashewar bom din ta lalata gine-gine da dama dake dab da gidan man.

'Yan sanda sun bayyana cewa, kafin fashewar bom din, masu kiyaye tsaro sun shirya yin bincike kan motar dake tsaye a kofar shiga gidan man, jim kadan kuma bom din ya fashe a cikin wannan mota.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China