in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kwamitin IOC ya yi bincike kan yanayin shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru na Beijing
2019-01-30 15:52:51 cri

Shugaban kwamitin wasannin Olympics ta duniya wato IOC Thomas Bach, ya yi bincike kan yanayin shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru na Beijing a yankin Yanqing dake birnin Beijing da birnin Zhangjiakou a ranar 29 ga wata.

Bayan da ya gama yin binciken, Bach ya nuna yabo ga kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru na Beijing domin ya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata. Ya yi nuni da cewa, an samu babban ci gaba wajen cimma burin sa kaimi ga mutane miliyan 300 da su halarci wasannin kankara. Yayin da yake yin binciken, ya gamu da yara da 'yan wasa da dama masu sha'awar wasannin kankara, sun burge shi sosai. Gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru na Beijing gasa ce ta farko da aka fara aiwatar da ajendar wasannin Olympics ta shekarar 2020 tun da aka nemi daukar bakuncin gudanar da gasar, wanda ya samar da sabuwar gudummawa ga ayyukan wasannin Olympics. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China