in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ebola na ci gaba da yaduwa a yankunan da aka fi fama da barazanar tsaro a DRC
2019-01-30 14:15:59 cri

Stephane Dujarric, kakakin MDD ya bayyana cewa, cutar Ebola tana ci gaba da yaduwa a yankunan da aka fi fama da barazanar tsaro a jamhuriyar demokradiyyar Kongo DRC.

Karkashin wani aiki na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da sauran hukumomin kasa da kasa, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, tawagogin kiwon lafiyar suna ci gaba da gudanar da ayyukan kokarin gina wani tsari na kai daukin gaggawa ga wadannan yankuna da cutar ke kara kamari.

Akwai rahotannin barkewar cutar Ebola kimanin 650 wadanda aka samu daga ranar 24 ga watan Janairu, a inda annobar cutar ta barke a DRC, akwai hasarar rayuka da aka samu kimanin 443 sakamakon tsananin cutar ga mutanen da cutar mai saurin kisa ta kama, in ji hukumar ta WHO.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China