in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da 'yan kasar Saliyo 1400 ne suka samu horo a Sin a 2018
2019-01-30 13:36:02 cri

Jakadan kasar Sin a kasar Saliyo Wu Peng ya bayyana cewa, sama da 'yan kasar ta Saliyo 1,400 ne suka samu horo a fannoni daban daban a kasar Sin a shekarar 2018.

Daga cikinsu, mutane 1,300 sun samu damammaki ne daga fannoni na rayuwa daban daban ta hanyar guraben karo ilmi da gwamnatin Sin ta samar, yayin da kuma akwai dalibai 100 da suke karatu a kasar Sin karkashin shirin ba da guraben karo karatu na gwamnatin kasar Sin, Wu Peng shi ne ya bayyana hakan ga mahalarta bikin bazara wanda aka shirya a cibiyar Confucius ta kwalejin Fourah Bay dake Freetown, babban birnin kasar.

Jakadan ya yi alkawarin ci gaba da hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu a bangarorin da suka shafi gina rayuwar al'umma.

He Mingqing, darkatan cibiyar Confucius ya ce, a cikin shekaru 6 da suka gabata, cibiyar Confucius ta shirya kwasa-kwasai a matakai daban daban, kuma ta kafa wasu bangarorin koyarwa guda 14, wadanda suka kunshi matakan karatu na 'yan kananan yara, da sakantare, da na koyon sana'a, da kuma matakin ilmin jami'a.

Ya ce, adadin daliban da aka yiwa rejista a cibiyar ta Confucius ya kai 5,000 a shekarar 2018.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China