in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana neman dala miliyan 848 domin tallafawa 'yan gudun hijira a Najeriya
2019-01-30 10:01:44 cri

MDD da hukumomin ba da agaji ga al'umma a Najeriyar suna bukatar taimakon kudi kimanin dala miliyan 848 don tallafawa gwamnati da kasashen dake karbar bakuncin 'yan gudun hijirar da rikici ya daidaita daga Najeriyar don gudanar da shirin tallafawa 'yan gudun hijirar na shekara guda, kakakin MDD ne ya bayyana hakan a jiya Talata.

Stephane Dujarric, ya bayyana wa 'yan jaridu ceewa, MDDr da huhumomin dake hadin gwiwa da ita, sun kaddamar da wani shirin bayar da agaji na shekaru 3 tsakanin 2019-2021, inda a cikin wannan shekarar ta 2019 kadai, ana neman dala miliyan 848 don aiwatar da shirin,

Ya ce, an kaddamar da shirin ne tare da wani shirin samar da agajin gaggawa na shiyyar Najeriya, inda ake neman dala miliyan 135 don aiwatar da shirye shiryen wadanda dukkansu za su tallafawa gwamnatin Najeriya tare da kasashen dake karbar bakuncin 'yan hijirar na Najeriya.

Dujarric ya ce, kungiyoyin agajin na Najeriya suna da burin tallafawa mutane miliyan 6.2 wadanda rayuwarsu ta shiga cikin mawuyacin hali sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

A cewar MDD, sama da mutane miliyan 1.8 ke rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira a Najeriya kadai, yayin da wasu 228,500 ke gudun hijira a makwabtan kasashe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China