in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake duba daftarin dokar zuba jarin waje
2019-01-29 17:11:41 cri

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wanda shi ne hukumar kolin kafa dokoki ta kasar, a yau Talata ya fara nazari kan daftarin dokar zuba jarin waje karo na biyu, wato wata daya ke nan bayan da aka kammala nazari kan daftarin a karo na farko, matakin da ya shaida niyyar kasar Sin ta kaddamar da dokar cikin sauri, wanda kuma zai kasance wani hakikanin mataki da kasar Sin ta dauka wajen kara bude kofa ga ketare.

Tushen manufar bude kofa ga kasashen waje ta fuskar tsare-tsare shi ne kwantanta ka'idojin kasa da kasa, da kuma dacewa da dokokin kasuwa na manyan kasashen duniya. Wannan ne tushen tsara daftarin dokar zuba jarin waje a kasar Sin, mai yiwuwa wannan doka za ta zama muhimmiyar doka game da jarin waje da za a zuba a kasar Sin, wadda za ta maye gurbin dokar kamfanoni masu amfani da jarin Sin da kasashen waje, da dokar kamfanoni masu amfani da jarin waje, da kuma dokar kamfanonin hadin gwiwar Sin da kasashen waje, kana za ta kasance tabbaci ga kasar Sin dake dacewa da ka'idojin kasa da kasa wajen kara bude kofa ga kasashen waje.

A matsayinsa na wani tabbaci a fannin dokoki, daftarin dokar zuba jarin waje ya tanadi cewa, aiwatar da manufar tafiyar da jarin waje da na cikin gida daidai wa daida da shirin fitar da jerin sana'o'i da ayyukan da za'a haramta zuba jari a kansu. Wannan ya nuna cewa, wadanda ba su cikin jerin sana'o'i da ayyukan da za'a haramta zuba jari a kansu, za a bai wa baki 'yan kasuwa dama daidai wa daida a yayin da suke kafa kamfanoni, ko habaka kamfanoninsu.

An kaddamar da shirin fitar da jerin sana'o'i da ayyukan da za a haramta wa 'yan kasuwan kasashen waje zuba jari a kansu a kasar Sin a shekarar 2013 a yankunanta na gwaji cinikayya maras shinge,, sa'an nan aka fara aiwatar da shirin a duk fadin kasar Sin a shekarar 2017. A bara kuwa, aka fara daukar sabbin matakan musamman na ba da izni ga 'yan kasuwan waje da ke da niyyar zuba jari a Sin. Lamarin da ya sa kawo yanzu dai, yawan ka'idojin da kasar Sin ta dauka na kayyade kasuwanci ga baki 'yan kasuwa ya ragu zuwa 48. Ko shakka babu, tanadin wadannan cikin daftarin dokar zubo wa kasar Sin jari ya ba da tabbaci ta fuskar doka ga muhallin zuba jari na kasar a fili yadda ya kamata.

H

ukumomin kafa dokoki na kasar Sin sun nemo ra'ayoyi kai tsaye daga wajen wasu cibiyoyin hada-hadar cinikayya da kamfanonin kasashen ketare dake nan kasar Sin, shirin daftarin kuma ya ba da amsa kan bukatu da damuwarsu. Ga misalin, game da wadancan manufofi daban daban da kasar Sin ta kaddamar don goyon bayan kamfanoni wajen neman ci gaba, suna dacewar kamfanonin da 'yan cinikayyar kasar waje suka zuba jari a kai. Kana kasar Sin ta ba da tabbaci ga kamfanonin jarin waje wajen yin takara cikin daidaito kan sayo kayayyaki da gwamnati take yi.

A fannin kiyaye 'yancin mallakar fasaha kuma, an kayyade cewa, kasar Sin za ta kare 'yancin mallakar fasaha na baki 'yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka samu jari daga ketare. Kana, kasar Sin za ta kiyaye masu mallakar fasaha da 'yancin masu mallakar fasaha yadda ya kamata, domin sa kaimi ga wadanda suke son habaka hadin gwiwar fasahohi bisa ka'idojin kasuwanci. An kuma jaddada cewa, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su tsara shirin hadin gwiwar fasahohi bisa ka'idar nuna adalci, a yayin da baki 'yan kasuwa suke zuba jari a kasar Sin, bai kamata hukumomin dake kula da harkokin kasa su tilastawa bangarorin da abin ya shafa mika fasahohinsu ba.

Domin aiwatar da dokar lami lafiya, daftarin dokar zuba jarin waje yana mai da hankali kan ka'idar adalci bayan da aka yi nazari kan ka'idojin kasa da kasa da abin ya shafa. Misali idan wata kasa ko wani yanki ya dauki matakin nuna rauni da bai dace ba kan kasar Sin, to kasar Sin za ta mayar da martani bisa hakikanin yanayin da ake ciki. Wato yayin da dokar ta ba da tabbaci ga hakkin halal na masu zuba jari na kasashen waje, a sa'i daya kuma ta rubuta cewa, kasar Sin za ta mayar da martani ga kasashe ko yankuna wadanda suka dauki matakin nuna raini ga jarin kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana nacewa ga manufar samun moriya tare yayin da ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, amma ba zai yiyu ta amince da cin zarafin da ake nuna mata ba.

Ban da wannan kuma, masu nazarin al'amuran kasa da kasa sun lura da cewa, ra'ayi na daukar matakin radin kai, da na kariyar ciniki, da sauran batutuwa sun sa yawan jarin da aka zuba wa wata kasa a duniya ya ragu da kashi 40% a farkon watannin 6 na bara. Yayin da yawan jarin waje da ake zubawa kasashe masu ci gaban tattalin arziki ya ragu da kimanin kashi 70%. Sai dai a nata bangare, kasar Sin ta samu jarin da aka zuba mata daga ketare da yawansa ya zarce kudin RMB Yuan biliyan 880 a shekarar 2018, adadin da ya zama mafi yawa a tarihi, wanda kuma ya karu da kashi 0.9% bisa na shekarar 2017. Cikin kamfanonin kasashen waje da suka kara zuba kudi ga kasuwannin kasar Sin har da kamfanin Tesla na kasar Amurka, da kuma BMW na kasar Jamus.

Bisa wannan yanayin da ake ciki, fitar da dokar zuba jarin waje a wannan lokaci, ba tabbatar da ganin kasar Sin ta kara bude kofarta ga ketare bisa dokoki da kuma ka'idoji kadai zai yi ba, har ma da kara wa baki 'yan kasuwa imanin zuba jari a kasuwannin kasar. Bugu da kari, za a iya taimakawa baki 'yan kasuwa wajen tsara dogon shirinsu na zuba jari a kasar Sin. Sakamakon haka, an yi hasashen cewa, kasar Sin za ta zama daya daga cikin yankunan da suka fi jawo jarin waje a duk fadin duniya. (Sanusi, Bello, Jamila, Maryam, Kande, Murtala, Bilkisu, Zainab, Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China