in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mazauna kauyuka da dama a nan kasar Sin na samun kyautatuwar zaman rayuwa sakamakon matakan kawar da talauci ta hanyar tallafin kiwon lafiya
2019-01-29 14:54:01 cri

Matsalolin fama da talauci da sake komowar talauci sakamakon kamuwa da cututtuka na addabar iyalai masu yawa dake fama da talauci a wasu kauyuka a nan kasar Sin. Kwanan baya, wakilinmu ya kai ziyara gundumar Chicheng na lardin Hebei dake da nisan kilomita sama da 100 da birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ya gano cewa, gundumar ta yi nazari kan tsarin ba da tabbaci kan kiwon lafiya sanadin talauci, da inshorar cututtuka masu tsanani, da tallafin aikin jinya, tare kuma da hada kan inshorar aikin jinya ta kasuwanci, hakan ya warware matsalolin da wasu mazauna kauyuka ke fuskanta na fama da talauci da sake komowar talauci sakamakon kamuwa da cututtuka.

Yanzu ga karin bayanin da abokiyar aikinmu Bilkisu ta hada mana.

Kauyen Duanmugou na gundumar Chicheng yana tsakanin duwatsu ne, yanzu akwai iyalai 235 a kauyen, kuma yawan al'ummarsa ya kai 640. Ya yi suna sosai saboda talauci, da rashin ruwan sha, mazauna kauyen kan tafi wuri mai nisa don dauko ruwa. Fan Wenbao, wani tsoho a kauyen da shekarunsa ya kai 75 a duniya, ya ce, yanzu zaman rayuwar mazauna kauyen ya samu kyautattuwa sosai,

"A da, babu isashen ruwa a kauyenmu, sai mun dauko ruwa daga gefen wancan dutsen dake da nisan kilomita 2.5, mu kan tashi da sassafe. A shekarar 1978, mun kaura zuwa nan dake kusa da hanyar mota, hakan muka samu sauki wajen sufuri. Babu bukatar a dauko ruwa daga waje, mazauna kauyenmu sun iya neman aikin yi a waje, ta yadda zaman rayuwarmu ke samun kyautatuwa sannu a hankali."

Sakamakon wasu dalilai, ciki har da muhallin halittu da rashin ingancin manyan kayayyakin more rayuwa, mazauna kauyen Duanmugou suna ta yin kokarin kawar da talauci. Gwamnatin wurin ma na daukar hanyoyi daban daban, don taimakawa mazauna don gaggauta kawar da talauci da samun waddata.

Yanzu, mazauna kauyen Duanmugou ba sa damuwa da abinci da tufaffi, kuma sun samu tabbaci wajen samun ilmin tilas, da kiwon lafiya, da kuma ingancin gidajen kwana, kana ana ta samun kyautattuwar manyan kayayyakin more rayuwa. Fan Wenbao ya ce,

"Kungiyar kula da aikin kawar da talauci dake zaune a kauyenmu ta haka mana rijiya, ta ajiye fitilar titi, da kuma gina filin al'adu, ban da wannan kuma sun gyara hanyoyin kauyenmu. Yanzu ana samun zaman karko da hadin kai a kauyenmu."

Game da yadda zaman rayuwar iyalinsa yake, Fan Wenbao ya ce, a 'yan watannin da suka gabata, matarsa ta kamu da ciwon kashin baya na kasa, har sun kashe kudin RMB sama da dubu 80 don yin tiyata. Ba su da karfin biyan kudin. Amma, saboda manufar kawar da talauci a fannin kiwon lafiya, kudin RMB dubu 10 da wani kawai suka kashe. Fan Wenbao ya ce,

"Mun kashe kudin RMB kusan dubu 90 don yin tiyata, yawan kudin da aka biya mu ya kai kimanin dubu 75, idan aka kara kudin mota da na abinci da dai sauransu, kudin RMB kusan dubu 10 kawai muka kashe. Yanzu, watanni 3 kenan matata ta samu sauki. Ko da yake ba ta iya yin aiki mai nauyi, amma ta na iya dafa abinci."

Mataimakin shugaban gundumar Chicheng Wang Yuhui ya yi bayanin cewa, a cikin masu fama da talauci na gundumar, wadanda ke fama da talauci sakamakon kamuwa da cututtuka ko nakassa sun kai sama da kashi 50 cikin 100. Bisa wannan halin da ake ciki, gundumar ta kara tattara kudi, don kaddamar da inshorar aikin jinya ta kasuwanci:

"A lokacin da aka yi rajistar mutane masu fama da talauci a shekarar 2015, an yi kididigar cewa, wadanda ke fama da talauci sakamakon kamuwa da cututtuka sun kai kashi 34 cikin 100, idan aka kara da wadancan masu fama da talauci sakamakon nakassa, za su kai kimanin kashi 50 cikin 100. Game da haka, bisa tushen inshorar kiwon lafiya daga tushe, da inshorar cututtuka masu tsanani, da kuma tallafin aikin jinya da kasarmu ta kaddamar, mun kara kaddamar da inshorar aikin jinya ta kasuwanci, hakan aka warware matsalar fama da talauci sakamakon biyan kudi da yawa don samun jinya." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China