in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan Sin ya isa Washington domin tattauna batutuwan cinikayya da tattalin arziki
2019-01-29 14:03:44 cri

Mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, ya sauka a birnin Washington D.C na kasar Amurka jiya Litinin da rana, domin halartar tattaunawar manyan jami'an kasashen biyu, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya.

Liu He, wanda mamba ne a hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban bangaren kasar Sin dake tattauna harkokin tattalin arziki da Amurka, ya jagoranci tawaga mai kunshe da mambobin manyan bangarorin tattalin arziki na gwamnatin kasar Sin zuwa tattaunawar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China