A wannan rana, shugaba al-Bashir ya sanar da tsagaita bude wuta a jihar South Kordofan yayin da yake halartar wani taron gangami da aka gudanar a birnin Kadoli, babban birnin jihar. Ya kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar tana maida hankali tare da yin dukkan mai yiyuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a dukkan fannoni a yankin.
Shugaba al-Bashir ya kalubalanci SPLM da ta shiga yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar don kokarin samun ci gaba mai dorewa a yankin. (Zainab)