Shugaban kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta kasar Turkiyya Kerem Kinik ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai mutane kimanin miliyan 135 wadanda ke bukatar taimakon jin kai a duk fadin duniya, ciki har da kashi 71 bisa dari wadanda ke zama a kasashe membobin kungiyar OIC. A waje guda kuma, daga cikin 'yan gudun hijirar da suka bar muhallansu sakamakon tashen-tashen hankali, akwai kashi 61 bisa dari wadanda ke zaune a yankunan kasashen kungiyar OIC.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar bada agaji ta duniya ta Red Cross Gilles Carbonnier ya bayyana cewa, kafa sabon kawancen zai taimaka ga tallafawa miliyoyin yara da tashe-tashen hankali da bala'u suka shafa a yankunan kasashen kungiyar OIC, tare kuma da inganta kwarewar kasashe membobin kungiyar ta fuskar samar da agajin jin kai.(Murtala Zhang)