in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kudin Amurka ta sanar da kakabawa kamfanin man Venezuela takunkumi
2019-01-29 11:03:54 cri
Ma'aikatar kudin Amurka ta sanar a jiya Litinin cewa, za ta garkamawa kamfanin man fetur na kasar Venezuela takunkumi.

A wata sanarwar da ta bayar, ma'aikatar kudin Amurka ta ce, kamfanin man fetur na Venezuela, mallakin gwamnati ne dake samar da kudin shiga da kudin ajiya na ketare ga kasar, inda ta ce za'a haramtawa kamfanin amfani da kadarorinsa dake Amurka, kana kuma za'a hana jama'ar Amurka yin kasuwanci da kamfanin.

Tuni a ranar 23 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da amincewa da Juan Guaido a matsayin shugaban kasar Venezuela na wucin gadi, wanda shi ne shugaban majalisar dokokin kasar, kana dan jam'iyyar hamayyar kasar. Har wa yau, Amurka ta ce za ta ci gaba da matsawa Venezuela lamba ta hanyoyin tattalin arziki da diflomasiyya.

A nasa bangaren, shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da yanke huldar jakadanci da Amurka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China