in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta kare kanta game da dakatar da alkalin alkalan kasar
2019-01-29 09:41:53 cri

Gwamnatin Nijeriya, ta kare matakin shugaban kasar na dakatar da alkalin alkalan kasar, bisa zargin kin bayyana wasu kadarorin da ya mallaka.

Ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed, ya shaidawa manema labarai jiya cewa, dakatar da Walter Onnoghen ta biyo bayan take dokar da'ar ma'aikata, kuma ba ta da nasaba da zabukan dake karatowa na watan Fabreru.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar da dakatarwar, inda kuma ya rantsar da mukaddashin alkalin alkalai a ranar. Matakin da ya janyo ce-ce-ku-ce daga ciki da wajen kasar.

Daruruwan lauyoyi na kungiyar lauyoyi ta kasar ne suka yi tattaki a jiya Litinin, yayin da a ranar Asabar da ta gabata babbar jam'iyyar adawa ta kasar PDP ta sanar da dakatar da yakin neman zaben shugaban kasa na tsawon raneku 3, duk don nuna adawa da dakatar da Mai shari'a Onnoghen.

Lai Mohammed ya ce, dakatar da mai shari'a Onnoghen, mataki ne da shugaban kasar ya dauka bisa tanadin kotun da'ar ma'aikata, wadda batun ke gabanta, kuma ba ta nuna wata alama ta mulkin kama karya ko cin zarafi kamar yadda wasu ke zargi ba.

Ana tuhumar mai shari'ar ne da amfani asusun banki na sirri dake dauke da miliyoyin daloli, wanda bai bayyana ba. Dakatarwar za ta shafe tsawon lokacin da kotun da'ar ma'aikata ta kasar za ta dauka kafin yanke hukunci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China