in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kyautata dokoki da ka'idoji domin tabbatar da kara bude kofarta ga waje
2019-01-28 17:12:54 cri

A yayin taron tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa na shekarar 2019 na Davos da aka shirya makon jiya, kasar Sin ta sake nanata niyya da kuma imaninta na kara bude kofarta daga dukkan fannoni ga ketare. A yau wata daya da ya gabata, a yayin taron kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kan aikin tattalin arziki, a karo na farko, an gabatar da cewa, a shekarar 2019, kasar Sin za ta kyautata dokoki da kuma ka'idojinta domin tabbatar da kara bude kofa mai inganci ga ketare maimakon cinikin hajoji da abubuwan da ake bukata domin raya masana'antu da ta yi a cikin shekaru 40 da suka gabata. Wannan ya alamta cewa, manufofin kara bude kofa ga ketare da kasar Sin za ta dauka za su shiga wani sabon mataki.

Cikin shekaru 40 da suka gabata, yayin da kasar Sin take kokarin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofarta ga ketare, ta yi amfani da fifikonta a fannonin samun dimbin ma'aikata, da makeken yankinta, da kasuwanninta masu girma, wajen janyo abubuwan da take bukata don raya masana'antu daga kasashe daban daban, ta yadda ta samu ci gaba matuka ta fuskar samar da kaya, da kuma gina birane. Zuwa yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya shiga wani sabon yanayi, inda ya karkata ga kokarin tabbatar da ingancin ci gaba maimakon mai da hankali kan saurin ci gaba kawai. Haka zalika, yanayin daidaiton da ake samu tsakanin tsare-tsaren tattalin arzikin cikin gidan kasar da wajen kasar, ya sa ba zai yuwu a ci gaba da dogaro kan janyo jari daga kasashen waje kawai ba. Saboda haka, don kara bude kofar kasar, ana buaktar kafa wani tsari mai kyau, don hada albarkatun tattalin arzikin kasuwannin cikin gidan kasar Sin, da wadanda ke wajen kasar. Wannan a zahiri yake: sabon tsarin da zai dace da yanayin dukkan ciki da wajen kasar Sin tushe ne ga yunkurin kasar na neman kara bude kofa da samun ci gaban tattalin arziki.

Hakika kasashe masu tasowa sun fi mai da hankali kan bude kofa ga ketare wajen fitar da kayayyaki, shi ma sakamako ne da aka samu bayan da manyan kamfanonin kasa da kasa suka zuba jari a kasashen, dalilin da ya sa haka shi ne, kasashe masu tasowa suna da arzikin 'yan kwadago da danyen kayayyaki da kuma kasuwar sayayya, su kan ingiza masana'antu da biranensu ta hanyar bude kasuwa. A gabashin Asiya, an lura cewa, kasashen yankin sun fi son mayar da tsoffin masana'antunsu zuwa ga sauran kasashen da suka fi koma baya, misali kasar Japan ta taba mayar da tsoffin masana'antunta zuwa babban yankin kasar Sin ko kasashen dake yankin kudu maso gabashin Asiya, amma an daina yin haka lokacin da kasashe masu ci gaba suka gamu da matsalar samar da kayayyaki.

Matsalar hada-hadar kudi da kasashen duniya suka gamu da ita a shekarar 2008 ta zama wani muhimmin lamari wajen daidaita tsarin shige da ficen abubuwan da ake bukata wajen raya masana'antu a duk duniya. Sakamakon rashin daidaito a tsakanin kasa da kasa a fannonin zuba jari da cinikayya, kasashe masu arziki sun sake duba manufofinsu na raya masana'antunsu, lamarin da ya sa suka dauki matakan ba da kariya a fannonin da suka shafi sake raya masana'antu, haraji, da cinikayya da ketare, a karshe dai, lamarin ya yi tasiri wajen kawar da tsarin kwata kwata. Kasashe masu tasowa suna janyo abubuwan da ake bukata wajen raya masana'antu daga wajen kasashe masu arziki, wannan ba zai zama yadda ake raya tattalin arzikin duniya a yau da kullum ba, a maimakon hakan ma dai, a kan gamu da katanga ta fuskar manufofi yayin da ake hadin kan tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa, musamman ma a fannin cinikayya.

Don gane wannan canje-canjen yanayin tattalin arziki a duk fadin duniya, ya kamata kasar Sin ta fidda sabbin matakai domin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje yadda ya kamata. Cikin shekaru 40 da suka gabata, bi da bi, kasar Sin take yin kwaskwarima a gida, ta kuma shiga kasuwannin duniya ta hanyar hada babban tsarin kasuwannin duniya da tsarin kasuwanni a gida. Bayan barkewar matsalar sha'anin kudi a shekarar 2008, kasar Sin ta fara zurfafa gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikinta, ta kuma dukufa wajen bude kofa ga waje ta hanyar yin gyare-gyare a fannin kafuwar yankunan 'yancin ciniki. A shekarar 2018 da ta gabata, Sin ta cimma nasarar gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar karo na farko wato CIIE a birnin Shanghai na kasar, wanda ya kasance muhimmin dandalin da kasar Sin ta kafa domin neman daidaito tsakanin manufofinta a fannin tattalin arziki da na kasa da kasa baki daya, lamarin da ya nuna babban taken kasar Sin wajen bude kofa ga waje.

A halin yanzu, bude kofa ga kasashen waje ta fuskar tsare-tsare da inganta hadin-gwiwa tare da sauran kasashe, muhimman ayyuka ne da kasar Sin za ta yi yayin da take kara bude kofarta ga kasashen ketare ta fannin tattalin arziki. Bude kofa ga kasashen waje ta fuskar tsare-tsare, ba taimakawa rage yawan kudin da ake kashewa wajen yin kasuwanci ba kadai zai yi ba, har ma da taimakawa musayar albarkatu daban-daban tsakanin kasuwannin cikin gida da na waje. Alal misali, tun da aka kafa yankin cinikayya maras shinge a birnin Shanghai a shekara ta 2013, kasar Sin ta aiwatar da manufar tafiyar da jarin waje da na cikin gida daidai wa daida da shirin fitar da jerin sana'o'i da ayyukan da za'a haramta zuba jari a kansu. A matsayin wani birni dake kan gaba wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, a shekara ta 2018, Shanghai ta bullo da wasu ka'idoji dari don fadada bude kofarta ga kasashen waje, wadanda suka shafi bangarorin tattalin arziki daban-daban, kuma an kafa kamfanin kera motoci na Tesla mai jarin waje a Shanghai, al'amarin da ya zama wata muhimmiyar alkibla ga bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin take yi a sabon zamanin da muke ciki.

A yayin da ake kokarin gudanar da ayyuka game da bude kofa a fannin tsare-tsare, ban da shigar da kasuwanni, kasar Sin ta kuma yi kirkire-kirkire kan wasu manufofi, ciki har da kyautata muhallin gudanar da cinikayya, don kai matsayin bai daya da muhimman kasashen duniya a fannomnin ka'idoji da tsare-tsare. Ga misalin, a shekarar bara, birnin Shanghai ya yi kwaskwarima a jere kan manufofi da tsare-tsare da yake bi bisa ma'aunin muhallin gudanar da cinikayya da bankin duniya ya sanar. A cikin jerin sunayen kasashe da aka sanar a karshen shekarar 2018, matsayin karfin takara na kasar Sin ya karu da maki 32 bisa na shekarar da ta wuce.

A matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin tana kwatanta ma'auninta da tsarin ka'idojin kasuwar kasa da kasa, a sa'i daya kuma, sauran kasashe su ma suna kwatanta ma'auninsu da tsarin kasar Sin. Kasashe masu tasowa da dama sun fara lura da ayyukan yin kwaskwarima da Sin take yi don samun bunkasuwa cikin sauri, da neman tsaida manufofin bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima dake dacewa da yanayinsu tare da raya masana'antunsu. Game da wannan batu, shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta kasance sabon tsarin harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Sin, wadda za ta sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakaninta da manyan kasashe masu tasowa ta hanyar bude kofa ga kasashen waje ta fuskar tsare-tsare. (Sanusi , Bello, Jamila, Kande, Maryam, Murtala, Bilkisu, Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China