in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a hadarin ballewar dam a Brazil ya karu zuwa 58
2019-01-28 15:42:43 cri

Hukumomi a kasar Brazil sun ce, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar hadarin ballewar dam a kasar Brazil ya karu zuwa 58 yayin da wasu mutanen 305 suka bace a kudu maso gabashin jihar Minas Gerais.

Daga cikin mutanen 58 da suka mutu, mutane 19 ne kadai aka iya gane su. Wadanda suka bace din sun hada da mazauna yankin da hadarin ya auku, da ma'aikata daga kamfanin hakar ma'adanai na kasar wato Brazilian mining company Vale, kamar yadda sashen kashe gobara na jihar Minas Gerais ya sanar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China