in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar Fatah ta Falasdinu ta bada shawarar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasar
2019-01-28 11:14:03 cri

Kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Fatah da Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ke jagoranta, ta bada shawarar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasar nan ba da jimawa ba.

Cikin wata sanarwa da ta biyo bayan taron da aka yi karkashin Mahmoud Abbas, kwamitin ya ce ya kamata sabuwar gwamnatin ta hada da jam'iyyun siyasa da mambobin kungiyar 'yantar da al'ummar Falasdinu (PLO) da kuma kusoshin Falasdinawa masu zaman kansu, wadanda za su maye gurbin gwamnati mai ci dake karkashin Firaministan kasar Rami Hamdallah.

Har ila yau, kwamitin ya bukaci a kafa wani kwamiti da zai kunshi shugabannin Jam'iyyar Fatah, wanda zai fara tattaunawa da tsagin PLO game da kafa sabuwar gwamnatin.

A tsakiyar shekarar 2014 ne aka kafa gwamnatin Falasdinu mai ci, bisa tanadin yarjejeniyar sulhu da aka cimma a Gaza, a gidan jagoran Hamas wato Isma'il haniyeh. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China