in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran da Turkiyya sun tattauna hanyoyin kewaye takunkuman Amuruka
2019-01-28 11:02:47 cri

Kasashen Iran da Turkiyya, sun tattauna kan hanyoyin da suka hada da cinikayya mai rangwamen haraji da irinta bani-gishiri-in-baka-manda, domin kirkiro cinikayyar moriyar juna tsakaninsu, yayin da Iran ke cikin takunkuman Amurka.

Yayin wani taron da ya gudana jiya a Tehran, shugaban cibiyar ciniki da masana'antu da hakar ma'adinai da aikin gona na Iran, Gholam Hossein Shafeie da Shugaban hadakar cibiyoyin masana'antu da musayar kayayyaki na Turkiyya, Rifat Hisarciklioglu, sun kuma tattauna kan wasu batutuwa dake jan hankalin kasashensu.

Shugaban cibiyar ciniki da masana'antu na Iran, ya bayyana cinikayyar bani-gishiri-in-baka-manda a matsayin hanyar fadada dangantakar cinikayya tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, cibiyoyin cinikayya na kasashen za su yi gagarumin tasiri kan habaka irin wannan tsari na cinikin kayyyaki da hidimomi.

Shi kuwa na kasar Turkiyya, maraba ya yi da kudurin da takwaransa na Iran ya gabatar, yana mai cewa samar da tsarin cinikayya irin na bani-gishiri-in-baka manda, shi ne mafita ga Iran da Turkiyya game da takunkuman Amurka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China