Yayin taron manema labaran da aka yi a ranar 25 ga wata, Wang Shengzu ya bayyana cewa, a halin yanzu, tattalin arzikin yana ci gaba da bunkasa cikin sauri a galibin kasashe masu samun ci gaban tattalin arziki. Amma raguwar bunkasuwar tattalin arziki a wasu manyan kasashe, zai bada taimako wajen magance wasu matsaloli, sakamakon saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu da bai dace ba.
Ya kara da cewa, bisa hasashen da aka yi, a bana, adadin karuwar tattalin arzikin kasar Amurka zai kai kashi 2.5%, bai kai 2.9% na shekarar 2018 ba. Kana, adadin karuwar tattalin arziki a kasashen Turai zai kai kashi 1.5%, bai kai 1.9% na shekarar data wuce ba. A kasar Japan kuma, adadin karuwar tattalin arzikinta zai kai kashi 1.1%, wanda ya wuce 0.9% na shekarar 2018. A kasar Sin kuwa, saurin bunkasuwar tattalin arzikinta zai kai kashi 6.2%, adadin da ya dace da halin da kasar take ciki. (Maryam)