An ce, taken taron a wannan karo shi ne, "dunkulewar duniya a zagaye na hudu, wato kafa tsarin duniya a zamanin juyin juya hali na masana'antu karo na hudu", manufar taron ita ce tattaunawa kan sabon tsarin raya kasa da kasa cikin lumana da amincewa da juna da dorewa. Wakila kimanin dubu 3 daga kasashen duniya sun halarci taron.
Mr Brende ya jaddada cewa, yana da muhimmanci ne wajen kafa tsarin duniya mai dacewa da yanayin da ake ciki don tinkarar kalubale, ana bukatar dukkan bangarorin da abin ya shafa su yi taro da tattauna tare, kuma dandalin tatttaunawa na Davos ya samar da wannan dama. Ya bayyana cewa, don tinkarar kalubale da juyin juya hali na masana'antu karo na hudu ya kawo, dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya zai ci gaba da yin amfani da fifikonsa a matsayin dandalin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, ta haka za a amfanawa jama'ar fadin duniya. (Zainab)