Zaunannen wakilin Sin dake hukumar WTO jakada Zhang Xiangchen ya bayyana a gun taron cewa, a halin yanzu, an shiga lokacin da ake fuskantar barazana kan tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban. Bisa wannan yanayi, bude shawarwari kan batun ciniki ta yanar gizo yana da babbar ma'ana ta musamman ga farfado da aikin yin shawarwari na hukumar WTO, da daga imani na bangarori daban daban kan tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da kuma raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya.
Zhang Xiangchen ya kara da cewa, Sin tana son sa hannu kan wannan sanarwa tare da taka muhimmiyar rawa wajen yin kokarin cimma burin da aka tsara. Sin tana son yin kokari tare da bangarori daban daban da yin shawarwari cikin adalci don cimma samun sakamako mai biya bukatun bangarori daban daban musamman kasashe masu tasowa. (Zainab)