Mr Beasley ya bayyanawa dan jarida na kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, taimakawa kananan iyalan manoma yana daya daga cikin fasahohin da Sin ta samu wajen kawar da yunwa. A nahiyar Afirka, manoma kashi 80 cikin dari kananan iyalan manoma ne, muhimmin aiki wajen kawar da talauci da yunwa shi ne daidaita matsalolin kananan iyalan manoma. A wannan fanni, ya kamata kasashen Afirka su koyi fasahohin kasar Sin.
A ganin Beasley, shawarar "ziri daya da hanya daya" tana da babbar ma'ana ga aikin kawar da talauci da yunwa a duniya. Ya yi nuni da cewa, a sakamakon rashin cikakkun ayyukan more rayuwa a nahiyar Afirka, an kashe kaso 40 cikin dari na kudin shiga daga aikin gona kan aikin jigila a tsakanin gonaki da kasuwa. An kyautata sharudan ayyukan more rayuwa ta hanyar aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" don rage kudin da ake kashewa a wannan fanni, ta haka za a taimakawa manoma wajen kawar da talauci. (Zainab)