in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya jaddada bukatar hadin gwiwar kasa da kasa don tunkarar sauyin yanayi
2019-01-26 15:51:14 cri

Jakadan kasar Sin ya bukaci kasa da kasa da su kara azama wajen yin hadin gwiwa tare da yin aiki tare don tinkarar matsalolin da annobar sauyin yanayi ke haifarwa zaman lafiya da tsaron duniya.

Da yake jawabi yayin taron muhawarar kwamitin sulhun MDD game da batun sauyin yanayi, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya bayyana cewa, sauyin yanayi yana janyo bala'o'i wadanda ke haifar da illoli ga yankuna daban daban na duniya, kana yana yin barazana ta fuskar samar da abinci, da albarkatun ruwa, da muhallin halittu, da makamashi, da kuma rayuwar bil adama baki daya.

Ya bayar da shawarawari uku game da yadda za'a tinkari kalubalolin dake shafar sauyin yanayi daga mahangar kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.

Da farko, wajibi ne a rungumi tsarin gamayyar kasa da kasa domin gudanar da ayyukan da za su kyautata rayuwar al'ummar kasa da kasa da makomar bil adama ta nan gaba.

Na biyu, Ma ya jaddada bukatar dake akwai na lalibo hanyoyin amfani da makamashi mai tsabta da wanda ba ya gurbata muhalli da kuma taimakawa ci gaba bisa yanayin da al'umma ke ciki.

Na uku, Ma ya ce dole ne a kiyaye banbance banbance dake tsakanin kasashen duniya, kuma a mutunta su, inda ya bukaci a yi amfani da ka'idojin girmama juna da samar da daidaito da kokarin sauke nauyin dake bisa wuyan juna.

Da yake kammala jawabinsa, Ma ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa game da batun sauyin yanayi, da tallafawa ci gaban kasashe masu tasowa da shawo kan kalubalolin da suka jibinci wannan fanni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China