in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta cika alkawarinta wajen karfafa yin gyare-gyare da bude kofa
2019-01-25 19:55:22 cri

Yau shekaru biyu ke nan, tun bayan da shugban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a taron shekara shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na Davos, inda ya jaddada aniyar kara ingiza yunkurin dunkulewar duniya a fannin tattalin arziki ba tare da kasala ba, a kokarin jagorancin bunkasuwar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Bayan shekarun biyu kuwa, an sake jin muryar kasar Sin a dandalin Davos, inda aka sake gabatar da dabarun Sin kan yadda ya kamata a rungumi damar dunkulewar duniya a zagaye na hudu, baya ga bayyana aniyar kasar Sin ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje daga dukkan fannoni.

Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya nuna a taron Davos na bana, cewar dunkulewar duniya a fannin tattalin arziki abu ne da duniya ta saba da shi a tsawon tarihin ci gaba, kuma dole ne a nemi dabaru masu dacewa wajen warware matsalolin da ke bullowa, yayin da ake hade tattalin arzikin duniya. Abin da kasar Sin ta yi shi ne, ta gudanar da abubuwanta da kyau sosai, wato ta mayar da batun neman bunkasuwa a gaban komai, da kara yin gyare-gyare daga dukkan fannoni, da ma bude kofa ga waje daga dukkan fannoni. Duk wadannan kalaman da ya yi, sun yi daidai da na shugaba Xi Jinping shekaru biyu da suka wuce, wadanda suka nuna yadda kasar Sin ta binciki sauye-sauyen duniya, da ma tinkararsu yadda ya kamata.

A halin yanzu dai, Bil Adama ya shiga zamanin juyin juya hali na masana'antu karo na hudu, da dunkulewar duniya a fannin tattalin arziki a zagaye na hudu. Lamarin da ya bukaci a yi amfani da sabbin fasahohi na fasahar sadarwa, da tafiyar mota ba tare da matuki ba, da yin ciniki a Intanet da dai sauransu, bisa ra'ayin kara bude kofa ga juna, domin warware matsalolin karancin sabbin karfin ingiza ci gaban tattalin arziki, da rashin daidaiton ci gaba, da rage gibin kudaden shiga, baya ga nazari kan yadda ya kamata a yi amfani da damar dunkulewar duniya a zagaye na hudu. "Ya kamata a nemi dabarun rarraba waina yayin da ake habaka girmanta, kada a tsaya don yin rigingimu ba tare da katsewa ba kan dabarun raba wainar."

Game da wannan fanni, ya kamata a koyi fasahohin kasar Sin. Bayan da aka bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a kasar Sin a shekaru 40 da suka gabata, Sin ta kasance kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, kana kasa ta farko a duniya a fannin kera kayayyaki, da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, ta haka za a sa kaimi ga bunkasuwar ciniki a tsakanin kasa da kasa, da zuba jari ga kasashen waje, da kuma fadada kasuwa ga kasa da kasa.

Alal misali, Sin ta cika alkawarinta, da aiwatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima yadda ya kamata, kamar su yin kwaskwarima kan harkokin rundunar sojoji, da hukumomin gwamnatocin kasar, da rage buga haraji, da gudanar da bikin baje koli na kayayyakin da ake shigowa da su a kasar Sin karo na farko, da gabatar da sabon jerin sunayen jarin waje da aka amince da su, da kuma kara tabbatar da ikon mallakar ilmi ta hanyar shigar da tsari game da tarar kudi da yawa domin dakile sake aikata laifi, a cikin daftarin gyaran dokar lambar kira. Kamfanin Tesla ya kafa babban kamfanin kera motoci na farko a kasar waje a birnin Shanghai na kasar Sin, kamfanin BMW ya zuba jari da kafa kamfani na uku na kera motoci na kasar Sin a birnin Shenyang, kana kuma an kafa kamfanin hannayen jari na jarin waje irin sa na farko, da kuma kamfanin inshora na jarin waje na kasar Sin na farko a kasar Sin, dukkansu sun bayyana cewa, ana yin kokarin daukar matakai a duniya domin Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima da kuma fadada kasuwa. Wanda ya kirkiri dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya Klaus Schwab ya yi bayani cewa, gudummawar da kasar Sin ta samar ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya a shekaru 40 da suka gabata ta shaida cewa, bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima, hanya ce mafi dacewa wajen cimma burin samun wadata da bunkasuwa.

A halin yanzu, yayin da ake fuskantar kalubalen cinikin duniya da zuba jari, da hadarin faruwar ra'ayin bangarori, da ba da kariya ga cinikayya, da tunanin baiwa fararen hula ikon sarrafa siyasa, yadda za a yi don tinkarar dunkulewar duniya a fannin tattalin arziki a zagaye na hudu? Amsa shi ne a kara yin kokarin yin kwaskwarima, da bude kofa ga kasashen waje, da kafa tsarin duniya a zamanin juyin juya hali na masana'antu karo na hudu, bisa tunanin raya irin makomar dan Adam.

Wannan zabi ne na kasar Sin, shi ma alkawari ne da kasar Sin ta yi, domin cimma wannan burin, kasar Sin ta gabatar da manufarta a fannoni shida. Misali, ba da tabbaci ga tsaron daukacin bil Adama ta hanyar tsara ka'idoji da ma'aunin da suka dace, da mai da hankali kan moriyar kasashen duniya, musamman ma kasashen da suke samun saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa, da martaba ikon mulkin kasashe daban daban, ba tare da nuna fin karfin fasaha da tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, da nacewa ga tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, tare kuma da tsara tsarin fasaha irin na kwanciyar hankali da adalci da yin hakuri da juna, da sabon tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, kana, ya kamata a kiyaye adalci domin ba da tabbaci ga gudanar da aikin kirkire-kirkiren fasaha bisa tushen ka'idojin da kasashen duniya suke amicewa da su. Ban da haka, ya dace a kara kyautata manufofin kasa, domin ingiza wadata da kwanciyar hankali a fadin duniya.

An lura cewa, gwamnatin kasar Sin ta fi mai da hankali kan "ka'ida". Hakika a karshen bara, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, aiki mafi muhimmanci da za ta yi domin raya tattalin arzikin kasar shi ne ingiza bude kofa, da kara sayar da hajoji zuwa ketare, zuwa kara habaka kasuwa bisa ka'idojin kasa da kasa.

Yayin dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasashen duniya na bana na Dawos, sau tarin yawa kasar Sin ta ambaci kalmar "ka'ida", inda ta jaddada cewa, kasar Sin za ta nuna kwazo da himma kan aikin gyaran fuska kan tsarin tattalin arzikin kasar, ta yadda za ta daidaita huldar dake tsakanin adalci da riba yadda ya kamata, lamarin shi ma ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara mai da hankali kan ka'idojin kasa da kasa, da ma'auni da tsarin gudanar da harkokin cinikiyya mai inganci, yayin da take kokarin aiwatar da manufar bude kofa ga ketare, da haka nan kuma za ta kara kyautata aikin gudanar da harkokin kasa daga duk fannoni.

Daga matakan da kasar Sin ta dauka, da kuma sakamakon da ta samu tun bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis na kasar Sin karo na 18, an tabbata da cewa, ko shakka babu kasar Sin za ta cika alkawarin da ta dauka. (Kande Zainab Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China