in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattawan Amurka ta ki amince da kudirin da jam'iyyar Democrat ta gabatar game da sake bude ma'aikatun tarayyar kasar
2019-01-25 14:54:05 cri

A jiya ne majalisar dattawan Amurka, ta ki amincewa da wani kudirin doka da jam'iyyar Democrat ta gabatar na neman sake bude ma'aikatun tarayyar kasar ba tare da sanya kudin gina Katanga tsakanin kasar da Mexico da fadar White house ta gabatar ba .

Shi dai kudirin wanda ya amince da kudaden sake bude hukumomin kasar har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu, yana bukatar amincewar 'yan majalisar dattawa 60 ne kafin ya samu amincewa, ya samu amincewar 'yan majalisa 52 ne, yayin da 'yan majalisa 44 suka nuna rashin amincewa.

Dukkan 'yan jam'iyyar Democrats dai sun amince da kudirin, yayin da 'yan majalisar Republican 6 da suka da Lamar Alexander daga jihar Tennessee da Susan Collins daga Maine, sai Cory Gardner daga jihar Colarado, da Johhny Isakcon na Georgia. Sauran sun hada da Lisa Murkowkski daga Alaska da Mitt Romney daga Nevada ne suka goyi bayan kudirin tare da 'yan jam'iyyar democrats.

Sai dai kuma 'yan majalisar dattawan bangarorin biyu sun zargi juna bayan kada kuri'un, kan dakatar da harkokin gwamnati da gaza cimma matsaya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China