in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi bikin ranar Ilmi ta duniya na farko
2019-01-25 11:11:36 cri
Babban sakataren MDD Antoni Guterres ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da muhimman ga harkar Ilimi,yayin da gwamnati a nata bangare ta tallafa da yin hadin gwiwa da samar da kudade.

Guterres ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar, yayin bikin ranar ilimi ta kasa da kasa na farko. Yana mai cewa, a kalla yara da matasa da baligai miliyan 262 ne ba sa makaranta.

Jami'in na MDD ya ce, duniya ba za ta lamunci yara da matasa da ba su da kwarewar da suke bukata ta yin takara a tattalin arzikin na karni na 21, ko mu bar rabin al'umma a baya ba. Ya ce idan har dukkan yara maza da mata suka kammala karantun sakandare, to za a kawar da mutane miliyan 420 daga kangin talauci.

Yayin da ake murnar irin rawar da harkar ilimi ta taka wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba, a watan Disamban shekarar da ta gabata ne, babban zauren MDD ya amince da wani kuduri, inda ya ayyana ranar 24 ga watan Janairun kowacce shekara a matsayin ranar ilimi ta kasa da kasa.

A sakonsa babban darektan hukumar Ilimi, kimiya da al'adu ta MDD(UNESCO) Audrey Azoulay, ya bayyana cewa, rana ce ta" sake jaddada muhimman manufofi".

Baya ga wadannan sakonni, hukumar ta UNESCO, da tawagogin din-din-din na kasashen Ireland, da Najeriya da Norway, da Qatar da Singapore, sun shirya wani biki mai taken, " Bikin ranar Ilmin kasa da kasa irinsa na farko" a hedkwatar MDD dake binrin New York.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China