in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei ya tantance Jami'ar Kenya a matsayin cibiyar nazarin harkokin sadarwa
2019-01-25 10:32:01 cri
Kamfanin harkokin sadarwa na Huawie na kasar Sin, ya amince da kasancewar jami'ar Katolika dake kasar kenya (CUEA) a matsayin cibiyar nazarin harkokin sadarwa da fasahar kere-kere ta zamani (ICT)

Da yake jawabi yayin bikin, mataimakin shugaba jami'ar ta CUEA Stephen Mbugua, ya yi maraba da hadin gwiwar, da fatan cewa, za ta taimaka wajen kara horas da daliban jami'ar ilimin nau'ra mai kwakwalwa.

Mbugua ya ce, an zabi jami'ar ce saboda tasirinta a wannan fanni, da kayayyakin da take aiki masu inganci da sauran muhimman abubuwa da ake bukata a wannan fanni.

Bisa ga yarjejeniyar fahimtar juna da sassan biyu suka kulla, yanzu kamfanin Huawei na kasar Sin ya amince tare da baiwa jami'ar iznin ba da horo da kwarewar aiki a hukumance ga dalibanta dake amfani da manhaja da kayayyakin kamfanin wajen samun horo.

Mbugua ya kuma lura cewa, hadin gwiwa da kamfanin na kasar Sin, zai taimaka wajen sanar da kwarewa a fannin fasahar sadarwar zamani a kasar Kenya da ma nahiyar Afirka baki daya.

A nasa jawabin, manajan kamfanin Huawei mai kula da horaswa da ba da takardar shaida, Su Shuqi, ya bayyana cewa, horaswar za ta taimaka matuka wajen cike gibin dake tsakanin jami'o'i da kamfanoni.(Ibrahim)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China