in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wutar lantarki da aka samar bisa nukiliya a kasar Sin ta karu a 2018
2019-01-25 09:59:13 cri
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, wutar lantarki da aka samar ta nukiliya a kasar ta karu a shekarar 2018, yayin da kasar ta kara girke wasu nau'rorin.

Hukumar samar da wutar lantarki ta kasar Sin CEC, ta ce a shekarar da ta gabata, an samar da wutar lantarki da ta kai Kilowatt biliyan 294.4, adadin da ya karu da kaso 18.6 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata. Kwatankwacin kaso 4.2 cikin 100 na bakin dayan wutar lantarkin da kasar ke samarwa, inda ta yi tsimin tan miliyan 90 na kwal, sannan ta rage tan miliyan 280 na sinadarin carbon dioxide dake gurbata muhalli.

Hukumar ta ce, a shekarar 2018, an kula da sassan injunan nukiliyar dake samar da wutar lantarkin kasar yadda ya kamata. A kuma shekarar da ta gabatan, kasar ta Sin ta fara amfani da wasu injuna guda 7, wadanda ke iya samar da wutar lantarkin da ta kai kilowatts miliyan 8.84.

A halin yanzu, injunan samar da wutar lantarki bisa nukiliya 45 ne suke aiki a kasar, wadanda ke iya samar da wutar da ta kai kilowatts miliyan 45.9, wadda ta kasance ta uku mafi girma a duniya.

Hukumar ta ce, ana nan ana gina karin wasu injuna guda 11, wadanda ake fatan za su iya samar da kilowatts miliyan 12.18 ma hasken wutar lantarki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China