Cibiyar za ta samar da hidimar taimakon lauya, yare da al'adu ga bakin dake shigowa kasar ke bukata a lokacin da suke zaune da ma yin tafiye tafiye a cikin kasar ta Sin.
Bugu da kari, cibiyar gudanar da tsarin tattaunawa, da karbar rahotanni na korafe-korafe, da samar da taimakon gaggawa da kimanta da kuma wallafa muhimman bayanan gargadi a fannin tafiye-tafiye.
Hukumar NIA ta kuma bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, za ta kaddamar da wani tsari ta yanar gizo da wata manhajar wayar salula, wadanda za su baiwa jama'a damar gabatar da bukatar neman takardun shiga ko fita daga kasar da biyan kudi da sanin abubuwan da ake bukata ta intanet da wayoyin salula na komai da ruwan ka.(Ibrahim)