in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana fatan za a daidaita rikicin Venezuela ta hanyar yin shawarwari
2019-01-24 20:41:16 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan yanayin siyasar da kasar Venezuela ke ciki yanzu, tana kuma fatan bangarori daban daban dake cikin kasar za su yi hakuri, kuma su yi hangen nesa, haka kuma su yi shawarwari bisa kundin tsarin mulkin kasar, ta yadda za su daidaita matsalar da kasar ke fuskantar ta hanyar siyasa.

Kaza lika kasar Sin tana goyon bayan kokarin da gwamnatin Venezuela take yi, na kiyaye ikon mulki, da 'yancin kai, da kwanciyar hankalin kasar. Kana har kullum kasar Sin tana aiwatar da manufar rashin tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, a don haka take nuna adawa da tsoma bakin sauran kasashe a cikin harkokin gidan kasar Venezuela, tana mai fatan kasashen duniya za su taka rawa da ta ce kan wannan batu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China