in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin za ta kara bude kofa ga ketare domin ingiza hadin gwiwar kasa da kasa
2019-01-24 20:23:13 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, har kullum kasar Sin na nacewa manufar gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, haka kuma tana nacewa manufar bude kofa ga ketare, ta yadda za a ingiza hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, tare kuma kafa tsarin tattalin arzikin duniya ba tare da wata rufa rufa ba.

An ce, babban jami'in ofishin MDD dake Geneva Michael Moller, ya karbi intabiyun manema labarai a Davos, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana ba da babbar gudumowa wajen kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban.

Hua Chunying ta bayyana cewa, yanzu yanayin da kasashen duniya ke ciki yana cike da rashin daidaito, kuma akwai rashin tabbas, a don haka ya kamata kasashen duniya su kara mai da hankali kan aikin kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban. Kaza lika kasar Sin tana fatan kara kokari tare da sauran kasashen duniya, domin kafa tsarin tattalin arzikin duniya ba tare da wata rufa rufa ba, haka kuma domin gina kyakkyawar makomar bil adama baki daya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China