in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tallafin da Sin ta bayar ya warkar da masu ciwon yanar ido a Burkina Faso
2019-01-24 14:37:19 cri

A watan Mayu na shekarar 2018, aka sake farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Burkina Faso, hakan ya bude wani sabon babi a tarihi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A cikin watanni takwas da suka gabata, kasashen biyu suka yi mu'amala a dukkan fannoni tare da gudanar da hadin kai irin na samun moriyar juna bisa tsari. Kwanan baya, tawagar aikin jinya ta farko ta kasar Sin da aka kafa bayan farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu ta kammala aikinta a kasar ta Burkina Faso, inda mutane sama da 100 ne aka yi nasarar yi musu tiyatar yanar ido.

Kasar Burkina Faso dake yammacin nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya fama da talauci da MDD ta sanar, babu isassun na'urorin samar da aikin jinya da magunguna, kuma tana ja baya a fannin fasahar aikin jinya. A ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 2018, tawagar aikin jinya ta farko da kasar Sin ta aika da ita ta isa Ouagadougo, babban birnin kasar Burkina Faso. Shugaban tawagar mista Wang Yong ya bayyana cewa,

"Wannan tawagar ta zo ne daga birnin Beijing, wadda ke hade da mutane 10. Bayan kokarin da muka yi na tsawon rabin shekara, mun aza harsashi mai kyau kan ayyukanmu a kasar Burkina Faso. Da farko, mun rattaba hannu tare da bangaren Burkina Faso kan wasu takardu da abin ya shafa bisa tsari. Na biyu, mun yi wasu ayyukan tiyata ta hanyar amfani da na'urorin samar da jinya da muka ba su. Na uku, mun inganta ayyukan jinya ba tare da biyan kudi ba."

A ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2018, wata kungiyar kwararru dake hade da mutane 10 da suka fito daga aisbitin ido a karkashin jami'ar horar da likitoci ta birnin Wenzhou ta kasar Sin ta iso birnin Ouagadougo don yin tiyatar yanar ido ba tare da biyan kudi ba ga masu ciwo na wurin. Ya zuwa ranar 5 ga watan Janairun na bana, 'yan kungiyar sun yi nasarar yin tiyatar yanar ido 146 a asibitin Tengandogo na birnin.

Jakadan kasar Sin dake Burkina Faso mista Li Jian ya bayyana cewa, an gudanar da wannan aikin bada tallafin samar da aikin jinya ne da nufin inganta hadin kai a tsakanin kasashen Sin da Burkina Faso a fannin aikin jinya da kiwon lafiya, wanda ya kasance wani gwaji ne mai kyau. Ya ce,

"Tun da aka sake farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Burkina Faso, bangarorin biyu sun samu saurin ci gaba a fannoni daban daban, musamman ma a fannin aikin jinya, wannan ne kuma ya zama wani fannin da za a dora muhimmanci a kai wajen gudanar da hadin kai a tsakanin kasashen biyu a nan gaba bayan aka farfado da huldar diplomasiyya a tsakaninsu. Gudanar da wannan aiki, ba kawai zai samar da hakikanin gajiya ga mazauna wurin ba ne, har ma zai taimaka wajen kara matsayin fasahar aikin jinya na wurin."

Baya ga haka, akwai kuma samar da tallafin na'urorin samar da jinya da wasu magunguna masu darajar sama da SEFA miliyan 200, don goyon bayan ci gaban aikin jinya na wurin. Shugaban Tengandogon Alecande Sanfo ya yi godiya sosai ga kwararrun nan da suka fito daga kasar Sin:

"'Yan tawagar kwararru da suka zo daga asibitin ido karkashin jami'ar horar da likitoci ta birnin Wenzhou sun bada tallafi ga asibitin Tengandogo, sakamakon fasaharsu ta yin tiyata mai inganci da taimakon kayayyaki masu daraja da suka ba mu. Ban da wannan kuma, sun bada horo ga likitocin wurin, hakan aka bada tabbaci ga asibitin Tengandogo wajen zama asibiti da ya fi babban matsayi a kasar Burkina Faso, lallai an samu nasara kan hadin kai a tsakanin kasashen Sin da Burkina Faso a fannin kiwon lafiya."

An ce, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta dauki nauyin aika da tawagar aikin jinya ta biyu zuwa kasar Burkina Faso bayan farfadowar huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, 'yan tawagar guda 9 dake kasancewar kwararru a sassan kula da masu kamuwa da cututtukan zuciya, da na jiyyar gaggawa, da na kula da marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali, da na fida a kirji, da na kula da masu jin ciwon ciki, da na kula da lafiyar kwakwalwa da dai sauransu, sun riga sun isa Ouagadougo a ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 2018. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China