in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta ayyana barkewar cutar zazzabin Lassa
2019-01-24 09:55:07 cri
Hukumomin a Najeriya sun tabbatar da cewa, kimanin mutane 60 ne suka kamu da cutar zazzabin Lassa. Haka kuma an ayyana barkewar cutar a wasu kasashen yammacin Afirka da dama.

Cikin wata sanarwa da cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta fitar a Abuja, fadar mulkin kasar, wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe, ta bayyana cewa, an ba da rahoton bullar cutar dake haddasa zazzabi mai tsanani a jihohin kasar a kalla 8 tun a watan Janairu.

Cibiyar ta NCDC ta yi kira ga 'yan Najeriya da kada su firgita game da samun rahoton karuwar bullar cutar, domin cibiyar ta bullo da matakan da suka dace na tunkarar cutar a kasar.

Babban jami'in cibiyar ta NCDC Chikwe Ihekweazu ya shaidawa manema labarai jiya cewa,cikin jerin shirye-shiryen matakan riga kafin wannan shekara da take dauka, cibiyar taimakawa jihohin kasar, da magungunan gaggawa da ake bukata, ta kuma tura tawagar kai daukin gaggawa(RRT).

A shekarar da ta gabata, cibiyar ta ba da rahoton mutuwar a kalla mutane 143 a sassa daban-daban na kasar sanadiyar zazzabin Lassa. An kuma ba da rahoton bullar zazzabin a jihohin kasar 22 gami da yankunan kananan hukumomi 90 a shekarar da ta gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China