in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan gida da na waje sun yabawa kasar Sin kan yadda take cika alkawarinta na bude kofa
2019-01-23 14:21:44 cri





A yayin da ake dab da bude taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na shekarar 2019, masana na kasar Sin da na wasu kasashen duniya suna ganin cewa, kasar Sin ta bayyana amincewarta da tsarin kasancewar bangarori da dama da kuma niyyarta ta inganta hadin gwiwar kasa da kasa bisa matakan da ta dauka.

Wani rahoton bincike da dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ya fitar a kwanan baya ya nuna cewa, daukacin al'ummar kasashen duniya sun amince da tsarin kasancewar bangarori da dama, kuma suna fatan a inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa tare da nuna kyamar yiwa moriyar wasu kasashe illa domin biyan bukatar kai. Tsohon karamin jakadan kasar Poland a birnin Shanghai na kasar Sin, kana masanin harkokin kasar ta Sin, Mr. Sylwester Szafarz yana ganin cewa, baya ga gudummawar da kasar Sin take bayarwa wajen kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ta kuma raba wa kasa da kasa nasarorin da ta cimma bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da ma sauran tsare-tsaren hadin gwiwa da kasashen duniya.Ya ce,"Kasar Sin ta kiyaye ingantacciyar hulda da kasa da kasa da ma kungiyoyin duniya da suka hada da kungiyar BRICS da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da sauransu. Kasar Sin ta tsaya kan gudanar da hadin gwiwa bisa tushen zaman daidaito, kuma yadda take hadin gwiwa da kasashen Afirka ya zama misali mai kyau, hadin gwiwar da ta ke gudana bisa ka'idar cin moriyar juna a maimakon mulkin mallaka, wanda kuma ya samar da tabbaci ga zaman lafiyar duniya a nan gaba."

A nasa bangaren, Mr.Xu Hongcai, mataimakin babban masanin tattalin arzikin duniya a cibiyar nazarin mu'amalar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin, ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta samu amincewa daga kasashen duniya bisa yadda ta kyautata yanayin kasuwancinta a cikin shekaru biyu da suka gabata. Ya ce,"Ya kamata mu lura da cewa, mun yi ta samun ci gaba a cikin shekaru biyu da suka gabata. A watan Yunin bara, mun gyara jerin fannonin da aka hana kamfanonin kasashen waje zuba jari a kai, kuma ana sa ran a watan Maris na wannan shekara, za a aiwatar da tsari na bai daya game da fannonin da aka hana, ma'ana, ba za a nuna bambanci a tsakanin kamfanoni masu jarin gida da masu jarin waje da ma kamfanoni mallakar gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu ba. Don haka, kasar Sin ta zama abin yabawa ta fannin samar da yanayin kasuwanci mai kyau. Rahoton da bankin duniya ya fitar game da yanayin da kasa da kasa ke ciki ta fannin harkokin kasuwanci ma ya nuna cikakkiyar amincewa ga kasar Sin a wannan fanni.

A shekarar 2018 da ta shude, kasar Sin ta kuma burge duniya da yadda ta yi kokarin daukar matakai na kara shigo da kayayyaki daga ketare. Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su daga ketare da ta gudanar karo na farko ya shaida niyyarta ta yin hadin gwiwa da takwarorinta a sassan duniya. Alkaluma na nuna cewa, a bara, yawan kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga ketare da wadanda ta fitar sun kai dalar Amurka triliyan 4.62, wanda ya kai wani matsayin koli a tarihi, kuma daga cikinsu, yawan kayayyakin da take shigo da su daga ketare ya zarce dala biliyan 2000, lamarin da ya kai ga rage gibin cinikin da ke tsakaninta da kasashen duniya da kaso 16.2%.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha jaddada cewa, "a maimakon rufe kofarta, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen duniya". Stephen Perry, shugaban kungiyar wasu kamfanoni 48 ta kasar Burtaniya yana ganin cewa, yadda kasar Sin ke bude kofarta da kuma shawarar "ziri daya da hanya daya" da ta bayar, sun samar da damar bunkasuwa ga kasashen duniya. Ya ce,"kasar Sin babbar kasa ce da ke shigo da kayayyaki daga ketare da kuma fitar da kayayyakinta zuwa sassan duniya, wadda ta samar da gudummawar da ta kai kimanin kaso 30% ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Sin dama ce ga duniya. A yayin da karin kasashen da suka hada da kasashen Afirka da na Latin Amurka ke shiga cikin shawarar ziri daya da hanya daya, babu wata kasar duniya da za ta samar da irin wannan dama."

Bayanai na nuna cewa, taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na wannan shekara zai mai da hankali matuka a kan bunkasuwar kasar Sin. Bisa ga ajandar taron, za a shirya wasu taruka na musamman game da harkokin kasar Sin, inda za a tattauna "shawarar ziri daya da hanya daya" da "hasashen tattalin arzikin kasar Sin" da kuma "yadda kasar Sin za ta ba da gudummawarta ga makomar kasuwanci a duniya".

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China