Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Yaounde, fadar mulkin kasar, yayin ganawa da wasu ministocin kasar guda 7 don tantance yanayin jin kai da ake ciki a yankunan biyu. Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, baya ga wancan adadi, akwai kuma iyalai 1,200 da suka koma gidajensu.
Ya jaddada cewa, wajibi ne sauran kungiyoyin bayar da agaji dake da niyyar taimakawa mutanen da suka rasa muhallansu, su nemi izni daga gwamnati, don gudun taimakon nasu bai fada hannu 'yan ta'adda ba.
Jami'in ya ce, tuni aka kafa cibiyoyin tsugunar da 'yan tawayen da suka aje makamansu. ( Ibrahim)