in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Davos
2019-01-23 10:52:58 cri
Jiya Talata ne, aka bude taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Davos na kasar Switzerland. Mahalarta taron za su tattauna kan yadda za a aiwatar da shirin "dinkulewar kasa da kasa a matsayi na 4" wanda zai mai da hankali kan kyautata rayuwar al'umma.

Kafin bude taron, asusun ba da lamuni na IMF ya gabatar da sabon bayani game da "rahoton hasashen tattalin arzikin duniya" a birnin Davos, inda ya sake rage hasashen da aka yi kan karuwar tattalin arzikin duniya na shekarar 2019 da na shekarar 2020 zuwa 3.5% da 3.6%. Shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa Klaus Martin Schwab ya bayyana a yayin bikin bude taron da aka yi a jiya da safe cewa, dunkulewar kasa da kasa ya taimaka wajen kubutar da mutane masu dimbin yawa daga kangin talauci. A halin yanzu, ya kamata bangarori daban daban su daidaita shirin dunkulewar duniya ta yadda za a kara mai da hankali kan kyautata rayuwar al'umma.

Daga ranar 22 zuwa 25 ga wannan wata, wakilai kimanin 3000 daga gwamnatocin kasashen duniya, kungiyoyin kasa da kasa, bangaren kasuwanci da masana da dai sauransu, za su tattauna kan yadda za a bullo da sabon salon neman dauwamammen ci gaban zaman takewar al'umma, bisa babban taken taron, wato "Dunkulewar duniya a matsayi na 4: Bullo da tsarin kasa da kasa a lokacin da ake aiwatar da gyare-gyaren masana'antun duniya karo na hudu". (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China