in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin UnionPay na Sin ya fadada ba da hidima zuwa kasashe da yankuna 174
2019-01-22 20:26:01 cri

Ya zuwa karshen shekarar 2018 da ta gabata, kamfanin UnionPay dake ba da hidima ta hada hadar kudade na kasar Sin, ya fadada ba da hidimar sa zuwa kasashe da yankuna 174 dake sassan duniya.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce, a halin yanzu kamfanin na samar da hidimar biyan kudade ta wayar hannu, a kasashe da yankunan waje 46. A daya bangaren kuma, kamfanin na UnionPay ya samu karin hada hada ta abokan huldar sa a shekarar da ta gabata, wadda darajar ta kai kudin Sin yuan tirliyan 120.4, kwatankwacin dalar Amirka tiriliyan 17.69, karin da ya kai na kaso 28.1 bisa dari a shekara guda.

Kawo yanzu, UnionPay ya kuma baiwa abokan huldar sa katuna kimanin miliyan 100, a kasashen waje da yankuna 50, ciki hadda wadanda suka amince su shiga shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, wanda hakan ya kara fadada ci gaban kasuwannin kasa da kasa.

Kamfanin mai helkwata a birnin Shanghai, na kan gaba wajen yayata manufar amfani da fasahar biyan kudade ta wayar hannu, ta hanyar amfani da manhajar Alipay da WeChat, a gabar da karin Sinawa ke rungumar salon biyan kudin sayayya ta wayoyin salula.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China