in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Canada da ta sako Meng Wanzhou nan take
2019-01-22 19:37:01 cri

Rahotanni na cewa gwamnatin kasar Amurka ta sanar da gwamnatin kasar Canada cewa, za ta gabatar da rokon mika Meng Wanzhou, babbar darektar kula da harkokin kudi ta kamfanin Huawei na kasar Sin ga kasarta a hukumance. Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana yau cewa, gwamnatin kasarta ta riga ta bukaci gwamnatin Canada da ta sako madam Meng nan take domin tabbatar da kare hakkin halal nata. A sa'i daya kuma, ta bukaci gwamnatin kasar Amurka, da ta gyara kuskurenta ba tare da bata lokaci ba, haka kuma ta soke umurnin kama madam Meng, tare kuma da kawar da bukatar mika Meng ga Amurka.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya yau, jami'ar ta bayyana cewa, sau tarin yawa, gwamnatin kasar Sin ta nuna matsayinta kan wannan batun, kasancewar duk mai hankali yana iya fahimta cewa, batun kama madam Meng Wanzhou, ba batun shari'a ne mai sauki ba, kuma idan gwamnatin Canada ta yi amfani da yarjejeniyar mika wadanda ake zargi da aikata laifuffuka tsakanin ta da kasar Amurka yayin daidaita batun, hakan zai take hakkin halal, da tsaro na 'yan kasar Sin. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China