in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahotannin da CNN ta ruwaito game da "zaman rayuwar" wata 'yar kabilar Uyghur karya ce zalla
2019-01-22 13:34:13 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a wajen taron manema labarai da aka yi jiya cewar, cikakken binciken da hukumomin kasar Sin suka gudanar, ya nuna cewa, rahotannin da kafar yada labarai ta CNN ta Amurka ta ruwaito dangane da wata 'yar kabilar Uyghur wadda aka tsare a gidan kaso a Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang, wadda har ma ta ga yadda wasu mata 'yan kabilar guda tara suka mutu kuma daya daga cikin 'ya'yanta ya rasa ransa a asibitin kula da yara na Urumqi, karya ce tsagwaronta. Madam Hua ta ce kasar Sin na fatan CNN za ta dakatar da ruwaito irin wadannan rahotannin karya marasa tushe balle makama, kuma tana fatan wasu 'yan majalisar dokokin Amurka za su mutunta gaskiyar abun dake wakana, tare da yin watsi da ra'ayin cacar baka, da daina shafawa gwamnatin kasar Sin kashin kaji game da manufofinta kan harkokin addini da jihar Xinjiang.

A kwanakin baya ne, kafar yada labarai ta CNN ta Amurka ta ruwaito labarin wata 'yar kabilar Uyghur mai suna Mihrigul Tursun gami da "abubuwan da ta ji ta kuma gani", inda ta ce, wai daya daga cikin 'ya'yanta ya rasa ransa a asibitin kula da kananan yara dake Urumqi na jihar Xinjiang ta kasar Sin, har ma ta ce ta ga yadda wasu mata 'yan kabilar Uyghur guda tara suka mutu yayin da ake tsare da ita a wani gidan wakafi dake Urumqi.

Game da wannan batu, Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta ce, 'yar kabilar Uyghur da ake kira Mihrigul Tursun, 'yar asalin gundumar Qiemo ce ta yankin Mongoliya na Bayingol mai cin gashin kansa dake jihar Xinjiang. A watan Agustan shekara ta 2010, Mihrigul Tursun ta auri wani dan kasar Iran a kasar Sin, daga bisani kuma a watan Janairun shekara ta 2012, ta auri wani dan kasar Masar a Masar. Mihrigul ta ce, a watan Afrilun shekara ta 2015, ta haifi 'ya'ya guda uku a kasar Masar, wato Muezi, da Muaizi da Ailinna. A watan Maris din shekara ta 2018, mijin Mihrigul ya bayyanawa ofishin 'yan sandan gundumar Qiemo cewa, Mihrigul Tursun ta riga ta samu takardar zama 'yar kasa ta Masar, kafin daga bisani kuma aka soke takardar zama 'yar kasar Sin ta Mihrigul a gundumar bayan sauraron ra'ayinta. A ranar 22 ga watan Afrilu kuma, Mihrigul Tursun da mijinta tare kuma da 'ya'yansu guda biyu sun bar kasar Sin da takardun fasfo na kasar Masar.

Game da furucin da ta yi na cewa wai ta ga yadda wasu mata 'yan kabilar Uyghur tara suka rasa rayukansu a gidan kurkukun Urumqi, Madam Hua Chunying ta bayyana cewa:

"Bisa bayanan da muka samu daga hukumomin jihar Xinjiang, an ce, a ranar 21 ga watan Afrilun shekara ta 2017, ofishin 'yan sandan gundumar Qiemo ta jihar Xinjiang ya kama Mihrigul Tursun bisa laifin tunzura rikicin addini da nuna bambancin kabilu. Amma daga bisani aka gano tana dauke da cuta mai yaduwa, don haka a ranar 10 ga watan Mayun shekarar, aka sake ta. Bayan tsare ta na kwanaki 20, Mihrigul Tursun ta samu cikakken 'yanci yayin da take kasar Sin. Haka kuma daga shekara ta 2010 zuwa 2017, ta yi tafiye-tafiye sau 11 tsakanin kasar Sin da kasashen Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Thailand da kuma Turkiyya. Wato a takaice, 'yan sandan birnin Urumqi ba su taba tsare Mihrigul a gidan kurkukun wurin ba. To, ta yaya ta bayyanawa CNN da taron 'yan majalisar dokokin Amurka cewa ta ga yadda wasu mata tara suka mutu yayin da ake tsare da ita a Urumqi, kana 'yan sanda sun kulle ta a cikin wani dakin kurkuku cike da mata sama da hamsin?"

Game da maganarta ta cewa wai daya daga cikin 'ya'yanta ya mutu a asibitin kula da kananan yara dake Urumqi na jihar Xinjiang, Madam Hua Chunying ta nuna sakamakon binciken cewar:

"Bisa binciken da muka yi, daya daga cikin 'ya'yan Mihrigul Tursun mai suna Muezi, ya taba kamuwa da cututtuka, kuma Mihrigul ta kai shi asibitin kula da kananan yara na Urumqi don ba shi magani har sau uku a shekara ta 2016. Daga baya a watan Afrilun shekara ta 2018, Mihrigul Tursun da mijinta sun bar kasar Sin tare da dansu Muezi dauke da fasfo din Masar. Game da danta dayan wato Muaizi, wanda ba shi da takardar zama dan kasar Sin, Mihrigul Tursun ta taho da shi daga kasar Sin zuwa kasar Turkiyya ne a watan Janairun shekara ta 2016, inda yayar mijinta ke kula da shi. Ba mu san halin da yake ciki yanzu ba, amma dole ne ita Mihrigul Tursun ta sani. Saboda haka, rahotannin da CNN ta ruwaito cewa wai daya daga cikin 'ya'yan Mihrigul Tursun ya mutu a asibitin kula da kananan yara dake Urumqi har ma ba'a gaya mata dalilin yiwa danta jinya da magani ba sam ba su da tushe balle makama, karya ce zalla."

Baya ga yin maganar karya ga kafar yada labarai ta CNN, Mihrigul Tursun ta kuma bayyana "abun da ta ji ta gani" a wajen taron kwamitin kula harkokin kasar Sin na majalisar dokokin kasar Amurka a ranar 28 ga watan Nuwambar shekara ta 2018, al'amarin da ya zama wata muhimmiyar shaida da wani dan majalisar dokoki wato Marco Antonio Rubio ya yi amfani da ita wajen bullo da manufofi da doka kan batun kare hakkin 'yan kabilar Uyghur.

Game da wannan batu, madam Hua Chunying ta ce, 'yan majalisar dokokin Amurka suna zargin gwamnatin kasar Sin gami da manufofinta kan harkokin addini bisa rahotannin karya da wata makaryaciya ta kirkiro, abun da ko ta yaya ba za mu amince da shi ba. Muna bukatar sauran 'yan majalisar dokokin Amurka su mutunta gaskiyar abun dake faruwa, da yin fatali da bambancin ra'ayinsu gami da ra'ayin cacar baka, da dakatar da duk wani yunkurinsu na shafawa gwamnatin kasar Sin kashin kaji kan manufofinta dangane da harkokin addini da jihar Xinjiang. Idan har ba su daina irin wannan shirme ba, to mutuncinsu da na Amurka zai zube warwas.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China