Kungiyar ta ce, wannan shi ne harin kunar bakin wake na biyu da aka nufi kaiwa sojojin Amurkar cikin 'yan kwanaki a yankunan dake karkashin ikon Kurdawa dake arewaci da arewa maso gabashin Syria.
Rahotanni na cewa, harin ya jikkata sojojin Amurka biyu baya ga dakarun SDF dake karkashin ikon Kurdawa biyar da suka rasa rayukansu, lokacin da wani dan kunar bakin wake na IS ya tayar da wata nakiya da ya dana a cikin motarsa a wajen yankin kudancin Hasakah.
Ko da a ranar 16 ga watan Janairun wannan shekara ma, an ba da rahoton mutuwar sojojin Amurka 4, sakamakon wata nakiya da aka auna a kan jerin gwanon sojoji a birnin Manbij na arewacin Syria dake karkashin ikon Kurdawa. A lokacin, an dora alhakin fashewar kan kungiyar IS.(Ibrahim)