in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taya sabon shugaban DRC murnar lashe zabe
2019-01-21 20:10:28 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana fatan alheri a madadin kasar Sin, ga zababben shugaban janhuriyar dimokaradiyyar Congo wato DRC Felix Tshisekedi.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan, tana mai cewa, kasar Sin na martaba zabin al'ummar janhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Kotun tsarin mulkin kasar dai ta tabbatar da nasarar da jagoran 'yan adawa Felix Tshisekedi ya samu, a zagayen zaben kasar na karshe.

A cewar uwar gida Hua, janhuriyar dimokaradiyyar Congo ta cimma nasarar gudanar da zaben shugaban kasa mai cike da tarihi, kuma al'ummar ta sun yi namijin kokari wajin tabbatar da hakan

Ta ce kasar Sin na fatan daukacin sassan masu ruwa da tsaki a zaben janhuriyar dimokaradiyyar Congo, za su ci gaba da aiki tare cikin kwanciyar hankali, da daidaito da ciyar da kasar su gaba, kana sassan wajen kasar za su tallafa, wajen samar da yanayin wanzuwar hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China