Adadin sabbin guraben ayyukan yi da aka samar a yankunan biranen kasar ya kai miliyan 13.61 a shekarar 2018, inda ya karu da sama da gurabe 100,000 wanda ya dara na shekarun baya kana ya zarce hasashen da gwamnatin kasar ta yi tunda farko.
Adadin a shekarar 2018 ya karu sama da miliyan 13 a cikin shekaru 6 a jere.
Binciken ya nuna cewa adadin marasa ayyukan yi a yankunan biranen ya kai kashi 4.9 bisa 100 a watan Disamba, inda ya ragu da 0.1 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin shekarar data gabata. (Ahmad)