in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron karawa juna sani game da hadin gwiwar masana'antu tsakanin Sin da Najeriya
2019-01-21 13:38:51 cri


A jiya Lahadi ne, aka shirya taron karawa juna sani dangane da hadin gwiwar masana'antu tsakanin Sin da Najeriya karkashin shirin shawarar " Ziri Daya da Hanya Daya" a birnin Lagos na tarayyar Najeriya, inda wasu shugabannin kamfanonin kasar Sin, da wasu shehunan malamai daga jami'u da cibiyoyin nazari na Najeriya, suka yi musayar ra'ayi kan yadda za a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin masana'antu, gami da aiwatar da matakai bisa shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya".

Karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Lagos ne ya karbi kabuncin taron karawa juna sani na wannan karo. Kana mahalarta taron sun hada da jakadan kasar Sin a Najeriya Zhou Pingjian, da karamin jakadan kasar Sin dake Lagos Chao Xiaoliang, da gwamnan jihar Edo ta Najeriya Godwin Obaseki, da mataimakin gwamnan jihar Ekiti Bisi Egbeyemi, gami da sauran manyan kusoshi na wasu kamfanoni da jami'un kasar.

A cikin jawabinsa, jakadan kasar Sin a Najeriya Zhou Pingjian, ya ce shekarar 2019 ita ce shekarar farko da Najeriya take kokarin daukar matakai bisa shawarar " Ziri Daya da Hanya Daya". Wannan shawarar kasar Sin ce ta kaddamar da ita, da nufin amfanar da jama'ar kasashe daban daban. Sa'an nan a wannan karo, za ta iya zama babbar manufar da ake bi wajen gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Najeriya. Sa'an nan jakadan ya yi tsokaci kan hadin kan kasashen 2 a fannin masana'antu, inda ya ce,

"Muna alfahari yadda ma'aikatun kasar Najeriya suke kokarin hadin gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin. Yanzu muna ganin ci gaban da aka samu a fannin raya masana'antu a Najeriya. A wannan fannin, kasar Sin kawar Najeriya ce, wadda za ta iya yarda da ita, da kuma yin hadin gwiwa da ita."

A nasa bangaren, gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatocin jihohin kasar daban daban dukkansu suna matukar sha'awar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar, kuma suna goyon bayanta sosai. Ya ce ya yi imanin cewa, ayyukan gina kayayyakin more rayuwa da zuba jari za su samu ci gaba a Najeriya albarkacin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Gwamnan ya kara da cewa,

"Shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya' da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar ta sa mu farin ciki sosai. Domin shawarar na da wani yanayi na musamman, kana ta shafi buri na samun walwala tare. Gudanar da hadin gwiwa karkashin shawarar zai haifar da alfanu ga dukkan Najeriya da Sin baki daya, kuma zai tabbatar da moriya ga wadanda ke yin hadin gwiwar."

A cikin nasa jawabin, Chao Xiaoliang, karamin jakadan kasar Sin dake Lagos, ya ce, Sin da Najeriya sun kulla yarjejeniyar hadin kai karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", yayin taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2018, wannan ya nuna cewa shawarar ta riga ta zama wata manufa mai matukar muhimmanci wadda za ta jagoranci hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen 2. Chao ya kara da cewa,

"A yayin taron kolin dandalin tattaunar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, an gabatar da manyan shirye-shirye guda 8 da za a gudanar don zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin Sin da Afirka, Wannan ya bayyana cikakken shirin da za a aiwatar don raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka, gami da Sin da Najeriya. Sa'an nan za a kara yin mu'amala tsakanin gwamnatoci, da 'yan kasuwa da masana na bangarorin 2 don neman hada shirye-shiryen da aka gabatar da matakan hadin gwiwar da ake dauka tsakanin Sin da Najeriya."

Duk a yayin taron, wasu manyan kusoshi daga kamfanin gine-gine na CCECC na kasar Sin, da Tung's Group, da kamfanin raya yankin ciniki cikin 'yanci dake Lekki, da jami'ar Lagos, da ta Nnamdi Azikiwe, sun tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda za a aiwatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da habaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya, musamman ma a fannin masana'antu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China