Sanarwar na zuwa ne bayan da Netanyahu ya isa kasar Chadi jiya da safe, ziyara ta farko da wani firaministan kasar Isra'ila ya taba kaiwa kasar dake da musulmi mafiya rinjaye.
Firaminista Netanyahu ya sanar cewa, baya ga dawo da huldar diflomasiya da kasar Chadi, Isra'ila za ta kulla hulda da wasu kasashen musulmi, amma kuma bai bayyana kasashen ba. Ya ce, wannan wani juyin-juya hali ne da suke gudanarwa a kasashen Larabawa da na musulmi.
Netanyahu ya yaba da kulla hulda da kasar Chadi, a matsayin misali na yadda Isra'ila za ta iya kulla hulda a nahiyar Afirka da gabas ta tsakiya, duk da tashin hankalin dake ci gaba da faruwa tsakaninsu da Falasdinawa.
Ziyarar da ya kai a kasar Chadi ta biyo bayan ziyarar aikin kwanaki biyu da Deby ya kai birnin Kudus ne a watan Nuwamban shekarar da ta gabata. A shekarar 1972 ne dai kasashen biyu suka katse hulda a tsakaninsu.
Galibin kasashen Larabawa da na musulmi dai ba su kulla alaka da kasar Isra'ila ba. (Ibrahim)