in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi bikin ranar dusar kankara ta duniya
2019-01-21 10:34:44 cri
A jiya ne kasar Sin ta gudanar da bikin ranar dusar kankara ta duniya gami da bikin zamiyar kankara ta yara ta duniya, inda yara suka baje kolinsu a filayen zamiyar kankara sama da 100.

An dai gudanar da bikin ne a filin zamiyar kankara na Thaiwoo dake gundumar Chongli na birnin Zhangjiakou a lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, birnin da zai karbi bakuncin wasan zamiyar kankara a gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za a yi a shekarar 2022.

Yara da matasa 500 ne suka hallara a Thaiwoo domin shiga wasannin dusar kankara daban-daban da sauran wasannin don murnar bikin tare da sanin al'adun gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu.

Wuraren wasannin dusar kankara 114 dake fadin kasar Sin ne suka gudanar da wadannan wasanni a lokaci guda a jiyan.

Tun watan Yulin shekarar 2015 bayan da birnin Beijing ya samu nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da zai gudana a shekarar 2022, kasar Sin take kara kokarin janyo hankalun jama'a na ganin sun shiga wasannin kankara da na dusar kankara.

Bikin ranar dusar kankara ta duniya, wani bangare ne na kamfel din da hukumar shirya gasar zamiyar kankara ta duniya ke yi, mai taken "Hada yara a filin dusar kankara" domin yayata wasannin dusar kankara a matsayin wasa mafi dacewa da lafiyar matasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China