in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka mutu sanadiyar fashewar bututun mai a Mexico ya karu zuwa 79
2019-01-21 09:53:14 cri
Ministan lafiyar jama'a na kasar Mexico Jorge Alcocer ya bayyana cewa, a kalla mutane 79 ne suka rasa rayukansu, wasu 81 kuma suka jikkata, bayan da wani bututun mai ya yi bindiga a jihar Hidalgo dake kasar Mexico.

Da yake karin haske yayin wani taron manema labarai, Lopez Obrador wanda ya kama aiki a ranar 1 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, ya bayyana cewa, gwamnati ba za ta dakatar da matakan da take dauka tun a karshen shekarar da ta gabata a yakin da take kan masu satar mai ba.

Wasu alkaluman gwamnati na baya-bayan nan na nuna cewa, a shekarar 2018 da ta gabata gwamnati ta yi hasarar dala biliyan 3, sanadiyar satar mai.

A ranar Jumma'ar da ta gabata da misalin karfe 7 na maraice agogon wurin ne dai wani bututun mai a unguwar San Primitivo dake yankin Tlahuelilpan ya fashe ya kuma kama da wuta. Wannan yana daya daga cikin hadari mafi muni da fashewar bututun mai a kasar ta Mexico ya haddasa a 'yan shekarun nan.

Koda a watan Disamban shekarar 2010 ma, mutane 30 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 52 kuma suka jikkata a jerin fashe-fashe dake da nasaba bututun mai guda biyu a jihar Puebla dake tsakiyar kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China