in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala aikin gine-gine na harabar bikin horti-expo na Beijing na 2019
2019-01-20 20:35:26 cri

Kwanaki kasa da 100 ne suka rage kafin a kira bikin baje kolin fasahohin aikin lambu na duniya na horti-expo na Beijing na shekarar 2019. Ya zuwa yau ranar 20 ga wata, an kammala dukkannin manyan ayyukan gine-gine na harabar bikin, kana ana gudanar da ayyukan share fage lami lafiya.

Ya zuwa ranar kuwa, kasashe da kungiyoyi 110 sun riga sun tabbatar da halartar bikin, wadanda yawansu ya kai koli a tarihi. Haka kuma, yawan masu halarta masu zaman kansu daga cikin kasar Sin ya zarce 120.

Ana sa ran shirya bikin na horti-expo na Beijing a yankin Yanqing daga ranar 29 ga wata Afrilu zuwa ranar 7 ga watan Oktoba na bana.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China