in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun tsarin mulkin DRC ta amince da sakamakon zaben shugaban kasar
2019-01-20 15:55:37 cri

A daren jiya Asabar kotun tsarin mulkin kasar Kongo Kinsasha wato DRC ta sanar da cewa, ta amince da sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta sanar a ranar 10 ga wata, dan takarar jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi shi ne ya lashe zaben, kuma ya kasance sabon shugaban kasar ta DRC.

Kotun tsarin mulkin kasar ta gayawa kafofin watsa labaran kasar a daren jiya cewa, 'dan takarar wanda ya fito daga babbar jam'iyyar adawa ta demokuradiya da ci gaban zamantakewar al'umma Felix Tshisekedi ya samu kuri'u masu rinjaye, don haka shi ne ya yi nasarar lashe zaben.

Bisa dokar kasar ta DRC, kotun ce kadai ke da ikon yanke shawarar amincewa da sakamakon zaben.

An gudanar da zaben shugaban kasar ne a ranar 30 ga watan Disamban bara, daga baya hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben, inda aka bayyana cewa Felix Tshisekedi ya samu kuri'u kaso 38 bisa dari, yayin da Martin Fayulu 'dan takara na jam'iyyar adawa ta Lamuka ya samu kuri'un kaso 35 bisa dari, inda ya kai matsayi na biyu.

Bayan da aka sanar da sakamakon, an yi zanga-zanga sau tarin yawa a wurare daban daban a fadin kasar, domin nuna rashin amincewa da sakamakon, inda wasu ke zargin cewa, sakamakon ba na gaskiya ba ne, Martin Fayulu shi ma bai amince da sakamakon ba, har ya shigar da kara ga kotun tsarin mulkin kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China