in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afrika sun bukaci a dakatar da bayyana sakamakon zaben DRC
2019-01-19 17:24:21 cri
Shugabannin kasashen Afrika sun bukaci a dakatar da bayyana sakamakon karshe na zaben jamhuriyar demokradiyyar Kongo DRC, wanda aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba.

Shugabannnin gwamnatocin kasashen Afrika sun gudanar da wani babban taron tuntuba da yammacin ranar Alhamis a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika dake Addis Ababa.

Taron dai ya mayar da hankali ne game da halin da ake ciki a DRC tun bayan kammala zabukan shugaban kasa da na majalisar dokoki da shugabannin yankunan kasar, kamar yadda sanarwar bayan taron da aka fitar a ranar Juma'a ta tabbatar da hakan.

A ranar Alhamis aka bayyana dan takarar jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar ta Kongo, yayin da ake tababa game da alkaluman zaben.

Shugabannin kasashe da gwamnatoci da suka halarci taron sun cimma matsaya cewa akwai babban shakku game da sahihancin kwarya-kwaryar sakamakon zaben, wanda hukumar zaben kasar ta yi ikirarin bayyanawa, bisa ga kuri'un da aka kada, a cewar sanarwar.

Shugabannin sun amince da tura wata babbar tawagar wakilai da suka hada da shugabannin kungiyar AU da sauran shugabannin gwamnatoci, da kuma shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU, domin tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a kasar Kongon, da nufin cimma matsaya don lalibo bakin zaren kaucewa fuskantar rikicin bayan zabe a kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China