Ban da wannan kuma, Guterres ya yi gargadin cewa, ya kamata kasashen duniya su tuna da tarihi, kada su manta da darussan da suka koya sakamakon yaduwar kalaman nuna kiyayya da suka dinga yaduwa a shekarun 1930. A cewarsa, "Kalaman nuna kiyayya barazana ce kai tsaye ga hakkin bil Adama da dauwamammen ci gaba da kuma zaman lafiya da tsaro."
Baya ga haka, Guterres ya waiwayi nasarar da MDD ta samu a bara a fannonin inganta tinkarar sauyin yanayi na duniya, da warware matsalolin 'yan gudun hijira da makaurata da dai sauransu. Game da kwaskwarimar da ake kokarin aiwatarwa ga tsarin MDD, ya ce, an riga an samu babban ci gaba a fannin, "duk abubuwan da muke yi a yanzu haka, abubuwa ne da muka taba yin alkawarin yin kwaskwarima a kansu." (Bilkisu)