A watan Yunin shekarar 2018, Donald Trump da Kim Jong Un sun yi shawarwari tare da sanya hannu kan hadaddiyar sanarwa a kasar Singapore, inda suka cimma matsaya kan "kafa sabuwar dangantaka a tsakanin Koriya ta arewar da Amurka", da "kafa tsarin zaman karko da zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya". Inda Trump ya yi alkawarin bada tabbacin tsaro ga Koriya ta arewan, a nasa bangaren, Kim Jong Un ya sake nanata aniyarsa na "kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya". (Bilkisu)